Shugaba Bush na shan matsin lamba akan sauyin dubaru a Iraki | Labarai | DW | 23.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush na shan matsin lamba akan sauyin dubaru a Iraki

Wani babban jami´in diplomasiyar Amirka ya nemi gafara bisa kalaman da yayi cewar manufar Amirka a Iraqi ta kasance ta nuna girman kai da wawanci. Kwana daya bayan an watsa wadannan kamalan a wata hira da tashar telebijin din Al-Jazeera, Alberto Fernandez ya nemi gafara a rubuce a cikin wata takarda da ya aikewa ma´aikatar harkokin wajen Amirka ya na mai cewa lale yayi tuntube harshe. A kuma halin da ake ciki shugaba GWB na kara shan matsin lamba da ya sake tunani game da dubarunsa a Iraqi bayan wata ganawa da yayi da kwamandojin sojin kasar. Wasu shugabannin jam´iyar democrats sun yi kira ga fadar White House da kada ta jira har sai bayan zaben majalisun dokoki nan da makonni biyu kafin ta bayyana sabon tsarin lokaci da ta tsarawa gwamnatin Iraqi da ta karbi ragamar tabbatar da tsaro a yankuna masu yawa na kasar.