Shugaba Buhari na soma ziyara a Faransa | Labarai | DW | 14.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Buhari na soma ziyara a Faransa

Makasudin wannan ziyara dai shi ne kara kulla dangantaka tsanain Najeriya da kasar Faransa musamman a fannin yaki da kungiyar Boko Haram.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na soma wata ziyarar aiki ta kwanaki uku daga yau Litanin a kasar Faransa. Makasudin wannan ziyara dai shi ne kara kulla dangantaka da kasar Faransa musamman a wannan lokaci da kasar ta Najeriya dama makwabtanta ke fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan tsagerun Boko Haram kamar yadda ofishin shugaban ya bayyana a jiya Lahadin .

Shugaban Najeriyar dan shekaru 72 zai kai wannan ziyara ce a kasar ta Faransa a bisa gayyatar takwaransa na wannan kasa Francois Holland kamar yadda mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya bayyana a wani jawabi da ya fitar ta shafin e-mail.

Cikin dai tawagar ta shugaban akwai mai ba shi shawara kan lamuran tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da wasu manyan jami'ai a ma'aikatar tsaro da ma'aikatar kudi da ta harkokin kasashen waje. Da misalin karfe biyar na wannan Litanin shugabannin biyu za su yi ganawa ta keke da keke a fadar Elysee, kafin daga baya su jagoranci wani taron manema labarai na hadin gwiwa.