Shirye-shiryen zabe a gabashin Jamus
September 11, 2017Talla
Wannan rangadi dai zai maida hankali ne kan yadda mazauna yankunan ke shirye-shiryen shiga zabukan gama-gari da za a gudanar a ranar 24 ga watan Satumba na shekara ta 2017.
Cikin muhimman abin da wakilan harsunan Afirka na DW za su maida hankali a yayin ziyarar sun hada da tasirin jam'iyun da ke takara ganin yadda ake samun 'yan Afirka da dama da suka yi karatu a wasu garuruwa da ke gabashin kasar musamman garin Leipzig.
Kuna iya rubuto mana dukkanin tambayoyinku kan abin da ku ke son sani a kan zaben na Jamus dama tsarin siyasar kasar a shafinmu na sada zumunta na Facebook.