Shirye-shiryen fafatawa a zaben Nijar zagaye na biyu | Labarai | DW | 28.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye-shiryen fafatawa a zaben Nijar zagaye na biyu

Bangaran masu mulki da na 'yan adawa a Jamhuriyar Nijar, na ci gaba da daura damara domin tunkarar zaben shugaban kasar zagaye na biyu,

Bangaren masu mulki da na 'yan adawa a Jamhuriyar Nijar, na ci gaba da daura damara domin tunkarar zaben shugaban kasar zagaye na biyu, bayan da hukumar zaben kasar ta bayyana sakamakon zaben da ya gudana na ranekun Lahadi da Litinin a kasar wanda ya bai wa Shugaba Mahamadou Issoufou da ke neman wa'adi na biyu babbar tazara.

Sai dai duk da cewa ya na dauke a gidan kaso, dan takarar da ya zo na biyu a zaben shugaban kasar Hama Amadou na cike da kwarin gwiwa ta samun saa a wannan zabe mai zuwa. Zaben wanda zai guda a ranar 20 ga watan Maris mai zuwa, ya kasance wani babban abun azo a gani wanda daga ko'ina aka zuba idanu domin ganin yadda zata kaya, tsakanin dan takara da ke daukr a gidan kaso bisa zagin gama baki wajan safarar jairrai da tsofon abokin sa na kawance da ya marawa baya a shekarar 2011.