Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin akwai batun dakatar da zanga-zangar kungiyoyi da mahukunta suka yi a Nijar. A Najeriya kungiyar kare hakkin Musulmi a Legas ta nemi bayanai game da halaccin amfani da hijabi tsakanin 'yan mata 'yan makaranta a jihar.
Zanga-zangar dalibai na dada daukar zafi a sassa dabam-dabam na kasar Indiya don nuna goyon bayansu ga dalibai mata musulmai da aka hana shiga aji da hijabi a kudancin jihar Karnataka da ke Kudu maso yammacin kasar.
Daliban jami'ar Yamai fadar gwamnatin Nijar, sun gudanar da zanga-zangar shekara-shekara ta tunawa da ranar da jami'an tsaro suka yi wa wasu daliban jami'ar kisan gilla bayan bude musu wuta yayin wata zanga-zangar lumana
A Jamhuriyar Nijar a karon farko tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane kuma wanda ya fafata a neman shugabancin kasar tare da Shugaba Mohamed Bazoum, ya bayyana a gaban sauran jagororin 'yan adawa.
Jamhuriyyar Nijar ta karbi bakuncin wani taron koli da zai mayar da hankali kan neman hanyoyin kare hakkokin yara mata da ke fuskantar tsangwama a tsakanin al'umma.