A cikin shirin za a ji cewa shugabannin 'yan kabilar Igbo sun dauki matakin aiwatar da ayyukan raya kasa a yankin a cikin wani shirin gamayya na gwamnatocin Jihohin yankinsu biyar, a yayin da a Jamhuriyar Nijar mazauna yankin Damagaram suka fara daukar matakan kariya daga illar da ke tattare da shigar sanyin bayan sauraren gargadi daga likitotin yankin.