A cikin shirin zaku ji cewar huldar tattalin arziki da batutuwan da suka shafi bakin haure da tsaro na daga cikin bangarorin da aka mayar da hankali a ganawar da aka yi tsakanin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo a birnin Berlin.Kasar Ghana dai na son a sake lale dangane da taimakon raya kasa da aka saba wa kasashen Afirka.