Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Cikin shirin za a ji kungiyar 'yan Shi'a a Najeriya ta ce lafiyar jagoranta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky na cikin mumunan yanayi. A Nijar za fara zaman shari'a ne kan wasu manyan laifuka a yankin Diffa.
Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci hukunta masu hannu a badakalar kamfanin sufurin jiragen sama na Nigeria Air da ya yi batan dabo jim kadan bayan kadammar da shi a Abuja
Kasa da sa'o'i 24 da shiga wani yajin aiki na sai baba ta gani a Najeriya, kungiyoyin kwadago sun dakatar da yajin aikin da ke shirin zama zakaran gwajin dafi ga makomar sabuwar gwamnatin kasar.
Yayin da ake shirye-shiryen kaddamar da zababbun shugabanni a Najeriya, kotunan sauraron kararrakin zabe sun fara sauraron bukatun soke zabe da aka shigar a gabansu.
An fara sauraron shari'ar kararrakin zaben shugaban kasa a Abuja inda jamiyyu biyar ke kalubalantar nasarar zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu