1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta bijiro da wani sabon shirin tsaro

Ramatu Garba Baba
February 21, 2023

Kasar Chaina ta sanar da wani sabon tsari mai kunshe da wasu muhinman matakai da za su taimaka wajen inganta tsaro da kuma zaman lafiya a duniya.

https://p.dw.com/p/4NmTT
Saudi-Arabien Riad | Kronprinz Mohammed Bin Salman empfängt Xi Jinping
Hoto: Saudi Press Agency/REUTERS

A wannan Talatar, Chaina ta sanar da kammala wani sabon shiri kan harkokin tsaro da ta yi wa lakabi da Global Security Initiative ko GSI. Shirin ya shata wasu muhinman matakai da za su taimaka a tsaro da tabbatar da zaman lafiya a sassan duniya.

Ministan harkokin wajen kasar Qin Gang da ya baiyana fargabar rincabewar yakin Rasha da Ukraine na ganin wannan shirin zai yi tasiri a kokarin da ake na ganin bayan yakin da aka soma kusan shekara guda, ya baiyana cewa, kasarsa za ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya wajen samar da shawarwari da bude kafar tuntubar juna, domin magance matsalolin da ke damun dukkan bangarorin tare da nema wa juna mafita.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ke kara tsami a tsakanin Chaina da manyan kasashen yamma a sakamakon goyon bayan da ake zarginta da bai wa Rasha da ke mamayar Ukraine.