1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Talaka na da ta cewa kan dokar haraji?

December 31, 2025

Kungiyoyin fararen hula a arewacin Nijeria da ma al'ummar jihohin Katsina da Zamfara, na martani mai zafi kan sanarwar da shugaban kasa Bola Ahmed Tunubu ya fitar da kansa, game da dokar haraji da za ta fara aiki a 2026.

https://p.dw.com/p/56APh
Kudin Najeriya na Naira
Kudin Najeriya na NairaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Dagewar da shugaban na Nigeria Bola Ahmed Tinubu ya yi kan aiwatar da dokar harajin duk da cewar  al'ummar da suka zabe shi ba sa so, na ci gaba da tayar da kura a kasar ganin halin da al'ummar ke ciki na matsin tattalin arziki duk da shugaban kasar ya ce za su yi kyakkyawan amfani da kudin harajin.

Matsalolin da ake hange

Kudin Najeriya na Naira
Kudin Najeriya na NairaHoto: Ubale Musa/DW

Kwamared Jamilu Aliyu Charanci shi ne shugaban kungiyar Mutanan Arewacin Najeriya, na daga cikin masu ganin baiken dokar: "Ka ga wannan shi ke nuna maka shugabanni a Najeriya sun sauka daga turbar dimukuradiyya, sun koma kama-karya ko kuma mulkin mallaka. Sama da mutane milliyan 200 a Najeriya sun fito sun bayyana cewa, ba su amince da a ci gaba da wannan dokar ba......."

Akwai zarge-zarge da wasu 'yan majalisar kasar suka yi kan canza dokar harajin bayan kai wa majalisar kasar, abun da Kwamared Adamu Abubakar Kwatarkwashi shugaban wata kungiya da ke tallafawa al'umma a jihar zamfara ke cewa, hakan cin zarafin dimukuradiyya ne. A Najeriya dai an dade ana cece-kuce kan wannan doka har ta kai ga wasu kungiyoyin zuwa kotu, domin dakatar da dokar.

Abin da masana ke gani

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na NajeriyaHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Ko ya ya masana harkokin siyasa ke kallon hakan, ganin al'umma ba sa so amma mahukuntan sun da ge? Dakta Bishir Ibrahim Kurfi malami ne a jami'ar Umar Musa 'yar Adua da ke Katsina: "Wannan Gwamnatin tun da ta hau akwai tsare-tsareda dama da suka yi, kusan sun tsara su ne wajen wahalar da talaka a Najeriya. Tun daga lokacin aka cire tallafin man fetur, akwai alkawarin da shugaban kasa ya yi wa 'yan kasa da kusan har yanzu ba a aiwatar ba......."

Wasu masana tattalin arziki na cewa ko da yake gwamnati na da hujjar kara haraji domin samun karin kudin shiga da bunkasa ayyukan raya kasa, amma ya kamata a fara da rage barnatar kudi a kuma yaki cin-hanci da rashawa da kuma inganta hanyoyin tara haraji ba tare da cutar da talaka ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani