Biyan haraji abu ne da ya wajaba a kan kowane dan kasa na gari. Da wannan kudin gwamnatoci ke amfani wajen gudanar da ayyukan raya kasa.
Nau'o'i daban-daban ake da su na haraji, akwai wanda ake zaftara a cikin duk abubuwan da ake saye ko sayarwa, akwai kuma wanda ake biya daga dukiyar da aka tara.