Shekau: Inanan da lafiya ta | Labarai | DW | 05.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekau: Inanan da lafiya ta

Abubakar Shekau ya karyata sojojin Najeriya na cewa sun raunata shi, tare da halaka makusantansa, shugaban kungiyar Boko Haram ya bayyana ne a sabon bidiyo mai tsawon mintuna 14 da ya wallafa ta yanar gizo.

Nigerien Boko Harams Führer Abubakar Shekau (picture-alliance/AP Photo)

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shakau

A cikin wannan makon ne dai kakakin rundunar sojojin Najeriya Birgediya Janar Usman Kuka Sheka, ya sanar cewa akwai yuwar rundanar sojojin sun raunata wasu jiga-jigagan kungiyar Boko Haram, a wasu harare-hare ta sama da sojojin suka kai kauyen Balla da ke kusa da dajin Sambisa a jihar Borno.

To sai dai sabon bidoyon ya nuna Shekau zaune a tsakiyar wasu kwamandojinsa biyu, inda ya ke cewa yana nan lafiya lau, kuma ba wanda aka raunata a cikin mukarrabansa. Kawo yanzu dai ba bu tabbacin inda aka nadi sabon bidiyon, to amma Shekau ya yi bayanin cewa a jiya Alhamis ne ya yi jawabin nasa. Amma babu martani daga bangaren jami'an tsaro kan wannan sabon bidiyo.