Shekaru uku da sace ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 14.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru uku da sace 'yan matan Chibok

Mahukuntan Najeriya sun ce suna kan aikin neman kubuto da 'yan makarantar Chibok da Boko Haram ke garkuwa da su skeakru uku da sace su. A cewar ta sacen 'yan matan babban laifi ne da aka taba aikatawa kan 'yan kasar.

Yayin da ‘yan matan na Chibok ke cika shekaru uku a hannun mayakan na Boko Haram, gwamnatin ta Najeriya ta ce tana nan tana bin duk wasu hanyoyin hada bayanai da tattaunawa don ganin an samo wadannan ‘yan mata da ransu.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya bayyana sace ‘yan matan na Chibok, da cewar shi ne laifi mafi muni da aka taba aikatawa kan wasu ‘yan Najeriya.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekara ta 2014 ne dai mayakan Boko Haram suka kwashe ‘yan mata 276 a arewa maso gabashin Najeriya. Cikin watan Oktoban bara kungiyar ta Boko Haram ta sako 'yan mata 21 daga cikinsu bayan wasu 50 din da suka tsere tun farko.