Shekaru biyar da Merkel ta ce ″za mu iya″ | Siyasa | DW | 03.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru biyar da Merkel ta ce "za mu iya"

Shekaru biyar ke nan da shugabar gwamnatin Jamus ta furta wata kalma kan batun 'yan gudun hijira. Kalmar da aka bayyana da mafi tasiri a tsawon lokacin mulkinta. Wannan kalma dai ita ce: "Za mu iya."

Flüchtlingsfamilie Suleiman Tochter Lama (DW/V. Kleber)

Lama Suleiman 'yar kasar Siriya da suka samu mafaka a Jamus

AN dai bayyamna wannan kalma ta "za mu iya," ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin kalmar da ta taka muhimmiyar rawa wajen rarraba kawunan 'yan kasar, dangane da batun 'yan gudun hijira.

A shekara ta 2015 ne dai, Merkel din ta furta wannan kalma, kalmar kuma da aka ce ta yi matukar tasiri wajen kwararar miliyoyin 'yan gudun hijira cikin kasar mafi yawansu daga Siriya.

Kalmar "za mu iya" dai, ta kasance kalma mafi tasiri a iya tsawon shekarun da Angela Merkel ta kwashe kan shugabancin gwamnatin Jamus.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin