Shekaru 500 da tawayen da ya kafa ′yan Lutheran daga Katolika | Zamantakewa | DW | 31.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shekaru 500 da tawayen da ya kafa 'yan Lutheran daga Katolika

A ranar 31 ga watan Oktoba shekara ta 1517 wani limamin coci da ake kira Martin Luther ya wallafa shahararren kundinsa mai sadara 95 inda ya yi kakkausar suka ga cocin Katolika bisa wasu manufofi.

Ranar 31 ga watan Oktoba rana ce muhimmiya a Jamus da ke zama ma ranar hutu. Rana ce da ake bikin cika shekaru 500 cif da guguwar sauyi a cocin Katolika, guguwar da ta haifar da bara'a ta wasu mabiya karkashin jagorancin Martin Luther da suka ce sun balle daga darikar Katolika sun kuma kafa cocin bara'a ta masu ra'ayin sauyi ko kuma Reformation a Turance. 

A wannan rana dai 31 ga watan Oktoba shekara ta 1517 wannan limamin coci da ake kira Martin Luther ya wallafa shahararren kundinsa mai sadara 95 inda ya yi kakkausar suka ga cocin Katolika bisa wasu manufofi. Tarihi ya nuna cewa Martin Luther ya kafe wannan kundi a kofar majami'arsa ta waliyai da ake kira "All Saints Church" da ke tsakiyar birnin Wittenberg a Jamus.

Martin Luther ya soki lamirin cocin na sayar da takardar shaidar tsarkake zunubai. A ikirarin cocin a wancan lokaci dukkan mutumin da ya fanshi takardar hadayar cocin, shi da iyalansa za a yafe masu dukkan zunubansu tare kuma bada tabbaci na samun shiga Aljanna.

Bayan da aka kore shi daga cocin Katolika, Luther ya kafa cocin Bara'a ta Reformation ko kuma Protestant. Kuma mabiyansa ana kiransu mabiya darikar Lutheran.  A wannan zamani akwai mutane fiye da miliyan 800 da ke bin wannan tafarkin Bara'a a duniya. To amma a nan Jamus inda aka yanke wa darikar cibiya, yawan mabiyansa na raguwa.


Sai dai a cocin St. Mary da ke Wittenberg babban cocin da ta yi fice a birnin, babu wata alama da ta nuna cocin ta Protestant na fuskantar wata matsala a nan Jamus. Mutane kimanin 70 kan halarci cocin domin adduo'in rana, zaune a kan bencina, sukan yi ta rera kasidu da ayoyi daga bible.

Yawancin masu ibadar 'yan yawon bude ido ne. Ba tare da wata wahala ba, nan da nan ka ke iya banbance baki da 'yan gari. Kusan dukkaninsu na sanye da taguwa jaket da takalman motsa jiki da jakar kyamarar daukar hoto da kuma taswirar hanyoyi da unguwannin cikin birnin. Cocin St. Mary na daya daga cikin muhimman wurare da 'yan yawon bude ido suke kai ziyara a Wittenberg. A wannan wurin ne Martin Luther ya kan yi wa'azi. Babban taron adduo'i na farko na mabiyar darikar Bara'a ta 'yan Protestant a  Jamus an gudanar da shi ne a wannan wuri. Cocin dai na alfahari da kiran kanta tushen kawo tafarkin sauyi a koyarwar addinin Kirista.

Sauti da bidiyo akan labarin