1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Shekaru 50 da harin Olympics

Peter Hille SB/LMJ
September 5, 2022

Shekaru 50 ke nan da kashe wasu Yahudawa 11 da dan sanda daya a Jamus, yayin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya da aka gudanar a birnin Munich.

https://p.dw.com/p/4GRgf
Jamus, Munich | Olympia | Hari | Yahudawa
Tunawa da 'yan wasa Yahudawa da aka kashe shekaru 50 din da suka gabata a JamusHoto: Peter Kneffel/dpa/picture alliance

Kwanaki tara da fara wannan gasa a ranar biyar ga watan Satumba na shekara ta 1972 shekaru 50 ke nan da suka gabata, an kai hari ga Yahudawa. A daren biyar zuwa wayewan garin shida ga watan na Satumba gwamnati ta tura jiragen yaki na sama, inda wasu Falasdinawa suka yi garkuwa da 'yan wasa Yahudawa tare da mika wasu jerin bukatu da suka hadar da sakin Falasdinawa da ake tsare da su.mJiragen yakin biyu sun dauki maharan takwas da mutanen tara da suka yi garkuwa da su, inda jami'an tsaro suka mamaye wajen da 'yan wasan ke zama.

Kisa | Yahudawa | Olympic | Jamus | Munich | 1972
Maharan sun yi musayar wuta da jami'an tsaron JamusHoto: Göttert/picture alliance/dpa

Tun da fari dai mahukuntan Jamus sun shirya gamawa da maharan domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su, amma an samu akasi lokacin da maharan suka mayar da wuta da bindigogin da ke hannunsu. Wani bangare na dalilin shi ne, lokacin jami'an tsaron Jamus ba su da kwarewa kan ceto wadanda aka yi garkuwa da su. Sai dai nan da nan aka ci gaba da wasannin, babu neman ahuwa daga 'yan siyasa ko 'yan sanda. Shekaru 50 bayan wannan garkuwa da kisan tawagar Isra'ila lokacin gasar ta guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympic a birnin Munich na Jamus, har yanzu akwai masu ganin lokaci ya yi na karfafa tunawa da mutanen da harin ya ritsa da su.