Shari'ar 'yan kungiyar Al-Kaida a Jamus
November 13, 2014Talla
A shari'ar da aka yi wa membobi hudu da kuma magoya bayan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Kaida, kotun kolin jiha ta birnin Düsseldorf da ke jihar nan ta North Rhein Westfalia ta yanke wa 'yan tarzomar hukuncin daurin shekaru hudu da rabi zuwa shekaru tara a kurkuku. Mutanen da ake wa lakabi da 'yan kungiyar Al-Kaida a birnin Düsseldorf, an same su da laifin kokarin shirya kai munanan hare-hare a Jamus bisa umarnin kungiyar Al-Kaida. A shekarar 2011 aka cafke mutanen kuma aka tsare su bisa zama 'ya'yan wata haramtacciyar kungiyar 'yan ta'adda ta ketare. An tuhume su da shirya harhada bama-bamai.