1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sharhin Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Abdourahamane Hassane
March 15, 2024

Wasu daga cikin Jaridun Jamus sun yi tsokaci kan zaben shugaban kasa a Afirka ta kudu wanda za a yi cikin watan Mayu

https://p.dw.com/p/4dhDe
Jaridun Jamus
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

A ranar 29 ga watan Mayu ne Afirka ta Kudu za ta gudanar da zabbukan kasa masu mahimmanci, kamar yadda wani hasashe ya nuna cewa jam'iyyar ANC mai mulki za ta iya rasa rinjaye a karon farko tun bayan da ta hau karagar mulki bayan faduwar mulkin wariyar launin fata shekaru 30 da suka gabata.

A ranar 27 ga watan Afrilu, na shekara ta 1994, aka yi zaben dimokradiyya na farko a Afirka ta Kudu wanda aka samu kusan kishi 87 na wadanda suka halarci zaben tare da zabar Jamiyyar ANC karkashin jagorancin Nelson Mandela wanda ya samu kashi 62 na kuri'un da aka kada. To amma yau jam'iyyar ta ANC ba ta da tabbas na dawowa kan karagar mulki

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na jam'iyyar ANC
Hoto: Denis Farrell/AP Photo/picture alliance

Jaridar Tageszeitung ta ce wani hasashe na baya-bayan ya nuna cewar jam'iyyar ta gaza cin nasara akan matsalolin zamantakewa da suka tsananta a kasar.Talauci ya shafi sama da kashi 55 cikin 100 na al'ummar kasar sannan ga rashin aikin kashi 33 cikin dari tsakanin matasa da manya. .

Masu jefa kuri'a 9,000 daga birane da yankunan karkara daga kuma dukkanin kabilu na kara nuna kyama ga 'yan siyasa wadanda ake ganin daga cikin adadin na mutum 9,000 da ke zaune a yankunan ‚yan rabana ka wadata mu da kyar a samu kashi 40 na wadanda za su zabi jam'iyyar ta ANC saboda talauci ya kai musu karo kuma gwamnatin ta gaza yin wani abu

Sjojoji Guinea Conakry sun yi karfa-karfa sun dauki mataki wannan shi ne taken da Jaridar Zeit Online ta bude sharhinta da shi. Wacce ta ce. Gwamnatin mulkin soji ta kori dukkan ministoci har ma da kwace asusu da fasfo dinsu.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Guinea Mamady Doumbouya
Hoto: CELLOU BINANI/AFP/ Getty Images

Birgediya Janar Amara Camara, babban sakataren shugaban kasar Mamady Doumbouya ne ya sanar da wannan tsattsauran matakin na korar Firaminista Bernard Goumou da rusa majalisar ministocin gwamnati nan take. Kana aka  rufe iyakoki da dakatar da shige da ficce da rufe sararin samaniyarsu har aka samu yamutsin 'yan makaranta biyu suka mutu wadanda iyayensu suka dora alhakinsu a kan sojojin

Firaministan farar hula Goumou, wanda Doumbouya ya nada, yana kan karagar mulki tun watan Yulin  shekara ta 2022 ya bar matsayin haka kwatsam bai shirya ba amma mai ya faru? Wannan ita ce ayyar tambayar da jaridar Zeit Online ta Aza.

Shakar iskar 'yanci kamar yada janar Kamara ya bayyana. Shi ne cewar "Dole ne kasar ta kasance cikin 'yanci kashi 100 bisa dari ba tare da samun hannu Faransa a cikin al'amuranta ba

'Yan tawayen kungiyar M23 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Hoto: Moses Sawasawa/AP Photo/File/picture alliance

Alhassane Camara, shugaban dalibai a Université Mercure Internationale, ya ce yin hakan ya kasance a bayyane yake cewa Guinea yanzu ta shiga wani yanayi kyamatar kasahen yamacin duniya. Hasali ma da Faransa kamar yadda Burkina Faso da Mali da Nijar suka yi.

Kwango na kara zama sansanin yaki gada-gadan wannan shi ne taken da jaridar Frankfurter Allgemeine ta wallafa sharhinta a kai da cewar yaki ya yi wa garin Goma da ke gabashin Kwango zobe..

Sojojin Kwango sun yi korafi  game da harin da jirgin mara matuki daga Rwanda ya kai a Garin Goma da ke a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.Kungiyar 'yan tawayen M23 ta kewaye Goma gaba daya, inda suka mamayeta tare da toshe duk hanyoyin shiga muhimmin birnin don ciniki. Yanzu kai kayan abinci a garin sai ta jiragen sama sakamakon haka, farashin abinci da man fetur sun yi tashin gwauron zabi. Jaridar ta Frankfurter Allgmneine ta kare sharhinta da cewar tun da aka fara kai hare-hare ta jiragen sama wannan hanya ma ta sayen kayan abinci a Goma ta kusan tsinkewa