1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin 'yancin kai cikin yaki a Ukraine

August 24, 2022

A cikin yanayi na zaman makoki da jajircewa, Ukraine ta yi bikin ranar samun 'yancin kai watanni shida bayan mamayar Rasha a kasar. Wata sabuwar kasa da ke kara karfi ta bulla, a cewar Roman Goncharenko na tashar DW.

https://p.dw.com/p/4Fzbf
Ukraine Kyiv | Bikin Tunawa da Ranar Samun 'Yanci
Al'ummar Ukraine sun yi bikin tunawa da ranar samun 'yancin kai, cikin yaki da RashaHoto: Metin Aktas/AA/picture alliance

Roman Goncharenko ya bude sharhin nasa ne da ayar tambaya da wata 'yar jaridar Jamus ta wallafa a shafinta na Twitter: Shin me ya sa ban ziyarci wannan kasar kafin yaki ya barke ba?  Ta ji haushi cewa ba ta ga manyan biranen Lviv ko Odessa ba tare da shingen hanya ba. Wannan tambaya ce da mutane da dama daga kasashen yammacin duniya suka yi lokacin bulaguro zuwa Ukraine tun bayan mamayar da Rasha ta yi a watan Fabarairu, kama daga 'yan jarida da 'yan siyasa da ma'aikatan agaji da ke kasar a karon farko. Ukraine ba ta taba samun kulawa sosai ba tun bayan ballewarta daga Tarayyar Soviet a shekara ta 1991, damar da yakin da ya barke a kasar ya bayar a yanzu.

Karin Bayani: 'Yan jarida na Ukraine sun samu kyautar DW

Abokiyar aikin dai ta fadi gaskiya, a ganinta ta rasa abin da ba zai sake faruwa ba. Akwai abubuwa da yawa fiye da abubuwan da ake gani na yaki. Tsohuwar Ukraine din dai na mutuwa sannu a hankali, sakamakon ruwan bama-baman na Rasha: An yi asarar mutane da gidaje da masana'antu. Dangantaka mai kyau kusan ta 'yan uwantaka tsakanin Ukraine da Rasha, ba za ta sake kasancewa kamar yadda ta kasance kafin yakin ba. Tsamin dangantakar da ta fara tun bayan mamaye Crimea a shekara ta 2014, ba za ta zama mafi girma ba. Al'ummomin kasashen biyu, za su jima da kiyayyar juna a zukatansu. Ukraine ta yi bikin ranar samun 'yancin kai ranar 24 ga Agusta a karo na takwas a tsakiyar yaki, a wannan karon lamarin ya sha bamban da na baya kasancewar na musamman ne: Watanni shida ke nan tun da Rasha ta kaddamar da yaki a kan wannan kasa.

Goncharenko Roman DW
Goncharenko Roman na tashar DW

Barazana ga kasa da al'ummarta na da matukar muhimmanci, kamar yadda ya kasance shekaru 100 da suka gabata. A lokacin 'yan Bolsheviks sun jefa al'ummar Ukraine cikin takaici, a daidai wannan rana ta 'yanci. Shin tarihi ne ke neman maimaita kansa? Akwai alamun cewar Shugaba Vladimir Putin na da niyyar hakan. Rahotanni da ke fitowa daga yankunan Ukraine da Rashan ta mamaye dai, na nuni da cewar ana kokarin kawar da al'adu har da yarukan mutanen. Sai dai hakar Putin ta tarwatsa Ukraine, ba za ta cimma ruwa ba. Tuni shugaban Rashan ya fara gangami a kan tsohuwar Ukraine, yana ganin abu mai sauki ta fuskar tattalin arziki da soja domin Ukraine na da rauni a wannan bangaren.

Karin Bayani: Ko Kamaru ta yi tir da mamayar Rasha a Ukraine?

A siyasance akwai rashin jituwa da rarrabuwar kawuna, inda kasashen yamma ke goyon bayan wasu yankuna. Yawancin wannan zargi gaskiya ne, amma duk da haka babban kuskure ne. Bayan watanni shida, Putin yana mu'amala ne da sabuwar Ukraine da ke kunno kai. Duk da cewar an fara shirin sasanci a kasar, kutsen Rasha ya hanzarta komai. Sabuwar Ukraine tana saurin yin ban kwana ga duk abin da ya daure kasar da Rasha shekaru da yawa, kama daga yare da sunayen tituna da ma abubuwan tarihi. Mafi muhimmanci sabuwar Ukraine tana koyon kare kanta, kuma hakan na faruwa ne cikin sauri tare da taimakon kasashen yammacin Turai ba kamar yadda ya kasance shekaru 100 da suka gabata ba.