1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako hatsin Ukraine daga gabar ruwan Odesa

Zainab Mohammed Abubakar M. Ahiwa
August 1, 2022

A wannan Litinin ne jirgin farko makare da hatsin kasar Ukraine ya bar tashar jiragen ruwa na Odesa ta tekun Bahar Aswad inda zai fitar da abinci zuwa kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/4EyyE
Ukraine-Krieg Odessa | Frachtschiff Razoni verlässt Hafen mit Mais
Hoto: UKRAINIAN NAVAL FORCES/REUTERS

Yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine da ke watanni biyar da suka gabata dai ya dakatar da jigilar kayan abinci musamman hatsi daga Ukraine, wadda ke zama daya daga cikin kasashen da ke wadata sauran kasashen duniya da abincin da take nomawa. Wannan ya haddasa hauhawan farashin kayan abinci, batun da ya jefa kasashe matalauta cikin halin kunci na rayuwa.

Daya daga cikin matuka jirgin da suka dauki tsawon watanni makale a gabar ruwan na Odesa, Engineer Abdulla Jendi ya wallafa hotuna da ma bidiyon yadda jirgin ruwan ya janye daga tashar jiragen ruwan na Ukraine da sanyin safiyar wannan rana ta Litinin.

Sakatare Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana wannan mataki da aka cimma a matsayin wata nasara a yunkurin ceto al'ummar duniya da ke cikin barazanar yunwa saboda tsada da ma karancin cimaka.

Guterres ya yi fatan cewar jigin na Razoni, shi ne na farko cikin jiragen dakon kaya masu yawa da za su ci gaba da barin Ukraine, tare da kawo daidaito da zaman lafiyar da ake hankoro a wannan rikici da ya jefa duniya cikin tsaka mai wuya, musamman ma mutane masu rauni cikin al'umma.

UNO | Atomwaffensperrvertrag-Gipfel | Antonio Guterres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio GuterresHoto: Yuki Iwamura/AP Photo/picture alliance

"Jirgin dakon kaya dauke da masara sama da ton dubu 26 ya kasance jirgin kasuwanci na farko da ya tashi daga tashar jiragen ruwa na Odesa tun daga ranar 25 ga watan Febrairu. Ana saran zai iso wurin bincike a inda aka tanadar a kasar Turkiyya a gobe Talata 2 ga watan Augusta. Bayan an kammala binciken ne zai shige zuwa tashar karshe na Tripoli da ke Lebanon".

A nashi bangare duk da cewar ya yaba da matakin fara jigilar abincin, kakakin hukumar Tarayyar Turai Peter Stano, ya ce kungiyar EU na saran dukkan bangarorin za su martaba yarjejeniyar, ta hanyar barin Ukraine ta sayar wa kasashen duniya hatsin da ta noma.

Tun da farko dai shirin samar da abinci na duniya, ya tsara saye da kuma dakon ton dubu 30 na alkama daga Ukraine da jirgin ruwa na Majalisar Dinkin Duniya.

Masu nazarin lamura na yau da kullum dai na ganin cewar wannan matakin kadai, na iya taka rawa wajen sassauta farashin kayan abinci irinsu hatsi da alkama da dangoginsu.