Sharhi: Matsalar kyamar Yahudawa | Siyasa | DW | 10.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Matsalar kyamar Yahudawa

Mahalartar wajen ibadar Yahudawa a birin Halle da ke yankin gabashin Jamus sun tsallake rijiya da baya, bayan da wani mai akidar 'yan Nazi ta tsattsauran ra'ayin kyamar baki da kuma kin jinin Yahudawa ya kai hari.

Sama da Yahudawa 70 ne suka hallara cikin wani wajen bauta a gabashin Jamus, inda suke gudanar da addu'o'i da wakoki a yayin bikin ranar Yom Kippur, rana mai matukar muhimmanci a addininsu. Sai dai matakan tsaron da aka sanya a bakin kofar shiga wajen bautar, sun hana wani Bajamushe dauke da manyan makamai da da suka hadar da gurneti samun damar zubar da jini. Tilas mu tuna da ranar tara ga watan Oktoba na 2019.

Shekaru 80 bayan fara yakin duniya na biyu, inda Jamusawa suka hallaka Yahudawa sama da miliyan shida, har kawo yanzu tilas Yahudawa a Jamus su rinka tunanin rayukansu in har za su bayyana addininsu da kuma halartar wuraren ibadarsu.

Me hakan ke nunawa a kan Jamus? Kuma me hakan ke nufi in har matashi dan shekaru 27 zai dauki kansa da kamarar da ke like a jikin hular kwano lokacin da yake aikata kisa kuma ya watsa cikin wata tashar wasannin bidiyo games a kafar sadarwa ta Internet? Ya yi irin abin da makashin da ya kai hari a cocin Christchurch da ke New Zealand ya yi, kuma kafin ya fara harbi sai da ya yi magana da Turancin Ingilishi, yana mai cewa: "Yahudawa ne tushen dukkan matsaloli."

Bai kamata ba kuma tilas a dakatar da wannan wahalar. A dangane da haka muna mika sakon ta'aziyyarmu ga 'yan uwan mutane biyun da wannan makashi yai wa kisan gilla, wadanda suka kasance mace da namiji.  

Ines Pohl ta ce abu ne da bai kamata a kawar da kai ba: Duk da yake abu ne da bai samu karbuwaba, don kuwa da ya samu da ma, da tuni a wannan Larabar an yi asarar rayukan Yahudawa da dama a Jamus.

Pohl Ines Kommentarbild App

Pohl Ines babbar Editar DW wadda ta rubuta sharhin

Wannan kisan ya nuna bai kamata a rinka takaita alhakin kin jinin Yahudawa a kan masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulumci kadai ba. Wanda duk ya ce haka kuwa ya sheka karya ya kuma ki gaskiya. Wannan ya nunar da cewa tsaurara tsaro a wajen ibadun Yahudawa a Jamus na da matukar muhimmanci, duk kuwa da cewa kusan shekaru 75 ke nan da kawo karshen ta'addancin 'yan Nazi. A zahirin gaskiya akwai ayar tambaya ganin cewa ba a dauki matakan tsaro a wajen ibadun Yahudawan, a ranar da suke bikin Yom Kippur ba.

Hakan ya nuna cewa komai kankatar shaidar da aka samu da ke nuna goyon bayan kyamar Yahudawa, ya zama wajibi a dauki mataki a kanta tare da hukunta wanda ya aikata. Wannan ya hadar da kona tutocin Isra'ila da kuma cin zarafin wanda ya bayyana kansa a matsayin Bayahude ta hanyar sanya hula irin tasu.

Kyamar Yahudawa ba abu ne da ya kamata a saba da shi ba. Babu wata kyama da za a bayyana ta a masatyin 'yar kadan, a ko ina, kuma tabbas ba a Jamus ba.

Sauti da bidiyo akan labarin