Shakku a kan yaki da ′yan ta′addan IS | Labarai | DW | 10.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shakku a kan yaki da 'yan ta'addan IS

Rahotanni daga kan iyakar kasashen Siriya da Turkiya na nuni da cewa kungiyar IS na ci gaba da samun galaba a kokarin da take na kwace iko da garin Kobani da ke kan iyakar kasashen biyu.

Kawo yanzu dai an tabbatar da cewa mayakan na IS sun kwace akalla sama da kaso uku bisa hudu na garin na Kobani. Wannan dai ya sanya shakku dama aza ayar tambaya kan tasirin yakin taron dangi a kan kungiyar ta IS da Amirka ke jagoranta a kasashen Iraki da Siriya tun cikin watan Satumbar da ya gabata. A hannu guda kuma kasar Turkiya ta sanar da cewa abu ne da ba zai yiwu ba a tsammaci za ta kaddamar da hari ita kadai a kan iyakarta domin ta kare wani gari da ke zaman na Kurdawa kawai. Kawo yanzu dai Amirka da kawayenta da suka hadarda kasashe daga yankin Gabas ta Tsakiya sun yi barin bama-bamai ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama fiye da sau 130 domin dakile ayyukan kungiyar ta IS.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu