1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sha'awar koyon Jamusanci ga matasan Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 20, 2021

Burin matasa a kasar Beni shi ne zuwa Turai domin yin karatu, sai dai hakan na bukatar makudan kudi. Koyon sana'o'i ko kuma karbar horo, ka iya zama mafita. Sai dai akwai gagarumin kalubale na lakantar harshen Jamusanci

https://p.dw.com/p/3xkaa
DW Benin Ausbildung in Deutschland
Hoto: Katrin Gänsler/DW

A birnin Abomey-Calavi da ke yankin kudancin Benin, a nan ne ofishin babar cibiyar koyon Jamusanci mai suna "Spaß mit Deutsch" ta ke. Cikin matasan da ke koyon Jamusanci daga tushe a wannan cibiya, akwai Jospen Aikoun.Tun bayan da ya zana jarrabawarsa ta kammala makarantar sakandare a shekara ta 2019, Aikoun ya mayar da hankali wajen koyon harshen Jamusanci domin samun damar cika burinsa. A cewarsa burinsa tun yana dan karami shi ne, ya je Jamus domin yin karatu mai zurfi. A karshe Jospen Aikoun ya cimma burinsa, inda ya samu gayyatar karbar horo a matsayin jami'in jinya a gidan kula da tsofafffi na Nobilis da ke birnin Troisdorf mai makwabtaka da birnin Kolon. 

Jospen Aikoun matashi da ke koyon Jamusanci a Benin don samun damar koyon sana'a a Jamus
Jospen Aikoun matashi da ke koyon Jamusanci a Benin don samun damar koyon sana'a a JamusHoto: Katrin Gänsler/DW

"Yanayi ne na matukar farin ciki a gare ni. wannan shi ne karon farko da zan tafi Turai. Na yi matukar farin ciki, kuma na dan damu ganin cewa tilas in bar abokaina da dangina. Na dan sha wahala kafin samun wannan dama. Na nemi gurbi fiye da sau 10. Abin farin ciki ne da gidan kula da tsofaffi na Nobilis suka neme ni. "

A cewar Jospen Aikoun mahaifiyarsa ce ta kwadaita masa aiki a fannin lafiya, wanda dama yana so, kuma bayan ya samu wannan dama baki dayan danginsa sun yi matukar farin ciki kasancewar shi ne mutum na farko da ya samu damar zuwa Turai. Za dai a iya cewa a yanzu tunanin zuwa Jamus domin samun horo ko koyon sana'a sabon abu ne a tsakanin matasan kasar Benin. Amos Mayowa Atchoba na daga cikin masu koyar da harshen Jamusanci a cibiyar "Spaß mit Deutsch" ta koyon Jamusanci a Benin din, ya yi karin haske yana mai cewa:

Akwai rashin kwarewar aiki a tsakanin wadanda suka kammala karatun jami'a a cewar Vianet Lokossou
Akwai rashin kwarewar aiki a tsakanin wadanda suka kammala karatun jami'a a cewar Vianet LokossouHoto: Katrin Gänsler/DW

"A shekarar da ta gabata, mun fahimci akwai damar hada karatu mai zurfi da karbar horo ko koyon sana'a. Mun fahimci cewa samun gurbin karbar horo a Jamus, zai taimaka wa dalibanmu. Da farko mafi yawansu na son zuwa Jamus ne domin yin karatu. Bayan karbar horon ko koyon sana'a, mutum zai iya samun aiki. Wannan abin sha'awa ne. Wanda ke son yin karatu a Jamus na bukatar makudan kudi a asusunsa na banki. Ba abu ne mai sauki ba. Da horo ko sana'ar da mutum ya koya, zai ji dadi sosoi."

Atchoba ya yi digiri a harshen Jamusanci a jami'ar Abomey-Calavi, da ke zama jami'a mafi girma a kasar ta Benin. Wasu dai kan yi fatan komawa gida bayan sun kammala abin da ya kawo su Turai da kyakkyawan sakamako, haka abin ya ke ga Jospen Aikoun da ya ce yana da burin komawa gida.

"Na fara tunanin abin da zan yi. Da farko ina son in na koma kasata, in hadu da abokaina mu kafa kungiya domin kula da tsofaffi. Watakila daga bisani mu gina gidan kula da tsofaffi na kanmu." 

Mai shekaru 19 da haihuwa ya iso Jamus yanzu haka, inda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa "Komai yana tafiya daidai a nan."