Schulz: Yarjejeniyar CETA na nan daram | Labarai | DW | 22.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Schulz: Yarjejeniyar CETA na nan daram

Bayan ganawa da Ministar ciniki ta kasar Kanada shugaban majalisar Turai Martin Schulz yace yana da kwarin gwiwa za a cimma masalaha.

Shugaban majalisar tarayyar Turai Martin Schulz ya shiga tsakani a wani yunkuri na ceto shirin yarjejeniyar cinikayya tsakanin kungiyar tarayyar Turan da kasar Kanada da ake yi wa lakabi da CETA bayan da tattaunawa a tsakanin bangarorin biyu ta ci tura a ranar Juma'a. Ministar ciniki ta kasar Kanada Chrystia Freeland ta ce ta kosa da kwan gaba kwan baya da ke haifar da tarnaki wajen cimma yarjejeniyar. Sai dai shugaban majalisar dokokin tarayyar Turan Martin Schulz bayan ganawa da Ministar cinikin ta Kanada ya tabbatar wa da yan jarida cewa an dinke barakar kuma a mako mai zuwa za su rattaba hannu akan yarjejeniyar. Ya baiyana matsalar da cewa matsalar ce ta cikin gida kuma ya yi amanna za su warware takaddamar cikin ruwan sanyi.