Saudiyya ta yi kashedi ga kasar Iran | Labarai | DW | 19.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya ta yi kashedi ga kasar Iran

Ministan harakokin wajen Saudiyya Adel Jubeir ya ce kasarsa a shirye take ta yi amfani da karfi domin taka birki ga Iran game da katsalandan da take yi a kasashen Larabawa.

Kasar Saudiyya ta gargadi kasar Iran da ta canza tsarin siyasar mu'amalarta da kasashen yankin Golf da ta bayyana a matsayin irin ta mulkin mallaka. Ministan harakokin wajen kasar ta Saudiyya Adel Jubeir ne ya yi wannan gargadi ga kasar ta Iran a wannan Litinin lokaci wani taron manema labarai da ya gudanar tare da takwaransa na kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a birnin Riyad.

Ministan harakokin wajen kasar Saudiyyar ya ce kasarsa a shirye take ta yi amfani da karfin siyasa da na tattalin arziki dama na soja domin taka birki ga kasar ta Iran kan abin da ya kira katsalandan din da take yi a harakokin cikin gida na kasashen Larabawa na yankin Golf kamar Lebanan da Siriya da Iraki da Yemen.

Ministan ya kuma yi kira ga kasar ta Iran da ta janye sojojinta da mayakan Hezbollah na 'yan Shi'a daga kasar Siriya tare da dakatar da samar da makamai ga sojojin Bashar Al-Assad.