1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Saudiyya ta dakile harin Iran a mahakar man fetur ta Shaybah

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 12, 2026

Mahakar fetur ta Shaybah na kusa da iyakar Saudi Arebiya da Hadaddiyar Daular Larabawa kuma ke karkashin kamfanin Aramco

https://p.dw.com/p/5ADWA
Yadda jirgin dakon man fetur na Mayuree Naree Bangkok ya kama da wuta a mashigin Hormuz 11 ga Maris, 2026
Yadda jirgin dakon man fetur na Mayuree Naree Bangkok ya kama da wuta a mashigin Hormuz 11 ga Maris, 2026Hoto: Royal Thai Navy/ROPI/picture alliance

Saudi Arebiya ta sanar da kakkabo jirage marasa matuka biyu da aka kai mata hari zuwa mahakar man fetur ta yankin Shaybah a wannan safiya ta Alhamis, a daidai lokacin da Iran ke ci gaba da far wa sansanoni sojin Amurka na yankin Gabas ta Tsakiya.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron Saudi Arebiya ta wallafa a shafinta na X, ta ce sun dakile harin bayan lalata jiragen, kwatankwacin yadda ta harbo tarin jirage marasa matuka da suka nufi cibiyar hako man fetur din a ranar Laraba.

Mahakar man fetur ta Shaybah, na daura da iyakar Saudi Arebiya da Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma ke karkashin kamfanin Aramco, daya daga cikin manyan kamfanonin hada-hadar fetur a duniya.

Tun bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka fara kai wa Iran, aka fara fuskantar hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya, inda Iran din ta toshe mashigin gabar ruwan Hormuz mai matukar tasiri ga tattalin arzikin duniya.

Karin bayani - Yakin Gabas ta Tsakiya ya shafi harkokin wasanni

Wasu jiragen ruwan Iran makare da makamai sun kai hari kan wasu jiragen dakon tankokin mai guda biyu a gabar ruwan Iraqi da ke yankin Gulf, lamarin da ya haddasa mutuwar mutum guda bayan jiragen sun kama da wuta.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito ma'aikatar sufurin Iraqi na cewa ta samu nasarar kubutar da jami'ai 25 daga cikin ma'aikatan jiragen biyu, a yankin Farhan al-Fartousi.

Rundunar juyin-juya halin Iran ta sha nanata barazanar far wa duk wani jirgin ruwan dakon fetur da ya ratsa ta mashigin Hormuz.

karin bayani - Firaministar Italiya ta soki Amurka da Isra'ila kan yaki a Gabas ta Tsakiya

Switzerland ta sanar da rufe ofishin jakadancinta dake Tehran babban birnin kasar Iran, na wucin-gadi, sakamakon tsanantar yakin Iran da kawancen kasashen Amurka da Isra'ila. 

Matakin na Switzerland ya samu yabo da jinjina daga aminiyarta Amurka, kamar yadda ofishin jakadancin Amurka a birnin Bern ya sanar, yana mai godewa wannan sadaukarwa don kare kimar Amurka.

Jakadan na Switzerland a Tehran da mukarrabansa biyar sun fice daga Iran a ranar Laraba, tare da fatan sake komawa da zarar yakin ya tsagaita, tare da cewa kofa a bude take domin ci gaba da tattunawa da Iran da kuma Amurka a gefe guda.

Karin bayani - Iran ta kama 'yan leken asiri 30

Lebanon ta sanar da mutuwar mutane bakwai a tsakiyar Beirut babban birnin kasar, sanadiyyar harin da Isra'ila ta kai mata da sanyin safiyar wannan Alhamis.

To sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ce mayakan kungiyar Hezbollah ta kai wa harin a yankin na Ramlet al-Bayda, wanda ya halaka mutane bakwai tare da jikkata wasu 21, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta sanar.

A gefe guda Hezbollah ta sanar da kai hare-haren makamai masu linzami zuwa sansanin sojin Isra'ila na birnin Tel Aviv yau Alhamis.

Kairn bayani - Trump ya ce yakin Iran ya dab da kawo karshe

Kimanin mutane sama da 630 ne suka mutu a Lebanon tun bayan farmakin Isra'ila ta kai Lebanon, tare da raba wasu sama da 800,000 da gidajensu.

A baya bayan aka jiyo shugaba Emmanuel Macron na Faransa na kira ga Isra'ila da ta dakatar da kai hare-hare Lebanon.