1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kama masu leken asiri 30

Abdul-raheem Hassan
March 10, 2026

Gwamnatin Tehran ta kama wani dan kasar waje da wasu mutane 29 da ake zargi da yin basaja suna yi wa Amurka da isra'ila ayyukan leken asiri a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/5A83i
Shugaban sojojin Iran, Janar Amir Hatam
Shugaban sojojin Iran, Janar Amir HatamHoto: Iranian Army Media Office/AFP

Ma'aikatar tattara bayanan sirri ta Iran ta ce tana cigaba da tsare mutanen da ta kama a mastayin masu leken asiri na cikin gida da wasu jami'an kasashen Isra'ila da Amurka.

Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya, Iran ta sha zargin Isra'ila da hukumomin leken asiri na yammacin duniya a matsayin zagon kasa a cikin kasar, musamman a kan sojojinta da makaman nukiliya. Jami'an Isra'ila ba kasafai suke yin tsokaci kan irin wannan zargi ba.