Sarauniyar Ingila na ziyara a Jamus | Labarai | DW | 23.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarauniyar Ingila na ziyara a Jamus

Sarauniya Elisabteh ta Ingila za ta kai ziyara garuruwa uku cikii har da Frankfurt da Berlin babban birnin tarayyar Jamus

Sarauniyar Ingila Elisabeth da maigidanta Philip za su gudanar da ziyarar aiki daga yau talata da ke zama irinsa na biyar a nan Tarayyar Jamus. Baya ga Berlin babban birnin, agendar ta su ta tanadi ya da zango a birnin Frankfurt da kuma sansanin gwale-gwale ta Bergen-Belsen da ke cikin jihar Nidersachsen.

Babu dai wani tanadin ku zo ku gani da aka yi a Berlin in banda ka-ikawon al'umma a kofar Brandenbourg. A gobe Laraba ne dai sarauniyar da maigidanta za su fara aiwatar da rukunoni na ziyarar tasu.