Sana′ar sayar da nama a Katsina | Himma dai Matasa | DW | 10.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Sana'ar sayar da nama a Katsina

Wani matashi mai sana'ar sayar da nama wanda ya fara da gasa naman dubu goma ya habaka kasuwancinsa inda ya bude babban wuri kuma matasa 25 ke yi masa aiki.

Habaka wannan wurin sayar da nama dai ya ja hankalin wasu matasa da suka koma sana'ar ta fawa wanda a da bisa al'ada yin sana'ar fawa sai dan gado amma ganin rufin asirin da suke samu ya sa suna cigaba da wannan sana'a wadda matashin mai suna Bishir Mansho ya habaka. A hirar da ya yi da DW matashin ya ce daga cikin wanda ya ke aiki da su akwai masu wanda suka yi digiri a jami'a.

Wannan matashi dai ya ce mataki da ya dauka na habakawa tare da zamanantar da ita ta rufa masa asiri fiye da yadda ba a zato kana ta taimaka masa wajen tallafawa 'yan uwansa matasa wajen sama musu aikin yi inda ya kara da cewar ''Alhamdulillah mun gode saboda mun samu daukaka fiye da sauran masu sana'ar nama a cikin garin Katsina saboda abinda mutane ke sha'awar shi ake masu kuma shi dama kasuwanci idan ana yin shi to mutanen da ke saye su rinka yabawa to shine kara cigaban kasuwanci''