Bincike kan satar bayanai a Jamus
January 7, 2019Talla
Ministan zai gana da shugabannin ofishin lura da aikata manyan laifuka da na tsaron kafafen sadarwar Internet domin jin sakamakon binciken da suka gudanar da kuma hanyoyin magance matsalar, inda ya yi alkawarin sanarwa da al'ummar kasar batutuwan da suka tattauna yayin taron.
Wannan dai shi ne kutse mafi muni da ya taba faruwa a kasar. Masu kutsen dai sun saci bayanan 'yan siyasar kasar kuma suka watsa a shafin Twitter. Wadanda wannan lamari ya shafa sun hada da shugabar gwamnatin Jamus dain Angela Merkel da shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier da 'yan majalisu da 'yan jaridu da kuma wasu fitattun mutane.