Samame a wuraren da baki suka fi yawa a Kolon | Labarai | DW | 21.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Samame a wuraren da baki suka fi yawa a Kolon

'Yan sanda a birnin Kolon na nan Jamus sun sake kai samame wuraren baki musamman shagunan da bakin 'yan arewacin Afirka suka fi zuwa.

Da yammacin ranar Laraba 'yan sanda a birnin Kolon Jamus sun sake kai samame a wata unguwa da ke gabashin birnin inda akasari baki ke da zama. Kimanin jami'an 'yan sanda 100 ne aka girke don gudanar da bincike a wurare hudu a unguwar Humboldt-Gremberg ciki har da wani wurin sayar da shayi da gidan abinci da shagon intanet da kuma wani shagon cacar pul. Kamar dai irin wannan samamen da aka kai ranar Talata a unguwar Kalk, an mayar da hankali ne kan masu aikata laifi masu asali daga kasashen arewacin Afirka da bakin haure. Dirk Weber shi ne kakakin 'yan sandan birnin na Kolon, wanda ya ce:

"Mun gudanar da bincike a shaguna hudu da ke a titin Taunus a unguwar Humboldt-Gremberg bayan bayanai da muka samu cewa wasu batagari kan nemi mafaka a irin wadannan shaguna bayan sun aikata laifi. Mun kuma samu bayanan cewa akwai bakin da ba su da takardun izinin zama a Jamus a wuraren."

'Yan sandan sun kame mutane da yawa a wannan samame. Tun bayan cin zarafin mata da ake zargin wasu 'yan asalin arewacin Afirka da hannu a birnin na Kolon ranar jajiberen shiga sabuwar shekara aka tsananta bincike kan bakin haure.