Saliyo ta samu cigaba a yaki da Ebola | Labarai | DW | 22.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saliyo ta samu cigaba a yaki da Ebola

Ma'aikatar kiwon lafiya a Saliyo ta ce lardin nan na Kailahun da a baya ya fi ko ina yawan masu Ebola yanzu ya zamto guda daga cikin wuraren da aka kawar da cutar baki daya.

Babban jami'in kiwon lafiya a lardin Sylvester Squire ya ce an shafe kwanaki 42 ba tare da an samu wanda ya kamu da cutar Ebola, lamarin da a hukumance ke nuna cewar an yi nasarar dakile bazuwar ta a wajen.

Shi dai wannan na Lardi na Kailahun musamman ma yankin Kissi Teng na daga cikin wuraren da aka fara gano cutar ta Ebola kuma ake zaton daga nan ne aka yada ta a sauran sassan kasar bayan da aka shigar da ita daga Gini.

Saliyo dai na daga cikin kasashen yammacin Afirka ukun nan da cutar ta fi yi wa ta'annaki inda a jimlace ta hallaka mutane 3145 yayin da wasu sama da dubu 10 ke dauke da kwayar cutar.