Saliyo na gab da kawar da cutar Ebola | Labarai | DW | 24.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saliyo na gab da kawar da cutar Ebola

An sallami mutum na karshe da ke dauke da cutar nan ta Ebola a Saliyo bayan da aka kammala yi masa magani kuma aka hakikance cewar yanzu bai dauke da kwayar cutar.

Ma'aiktar kiwon lafiya a kasar ta ce sallamar marar lafiyar yanzu na nufin babu wani sauran mutum da ke kwance a asibiti da sunan cutar ta Ebola wadda ta halaka mutanen da suka kai dubu hudu.

Yanzu haka dai kasar inji ma'aikatar kiwon lafiyarta ta ce ta shafe makonni biyu ba tare da samun wani da ya kamu da cutar ba, kana ta ce ta na daukar matakai na ganin ta kai ga kawar da ita baki daya.