Sabon harin bama-bamai a Maiduguri | Labarai | DW | 21.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin bama-bamai a Maiduguri

Ana fargabar mutane da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata bayan fashewar wasu bama-bamai guda hudu a yankin Gomari da ke Maiduguri fadar Jihar Borno a Najeriya.

Harin bama-bamai a Maiduguri

Harin bama-bamai a Maiduguri

Bama-baman dai sun tashi ne kusan lokaci guda da misalin karfe 7:40 na daren wannan Lahadi a wani wuri da ake kira Ajilari Railway da shataletalen Gomari kan hanyar zuwa filin jirgin sama na Maiduguri da kuma wani Masallaci. Ya zuwa yanzu dai ba a iya tantance harin na kunar bakin wake ne ko kuma an dasa ne ba. Wani da ya tsira daga harin mai suna Muhammad Al-Amin ya shaida wa wakilinmu na Gombe Al-Amin Suleiman Muhammad ta wayar tarho cewa harin da aka kai masallacin wata ‘yar kunar bakin wake ce ta tayar da bam da ke jikinta a dai dai lokacin da jama'a ke ficewa daga masallacin bayan kamala sallar Isha.

Ya zuwa yanzu dai babu yawan alkaluma na wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata sanadiyyar wadannan jerin hare-haren da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai.