Sabanin ra′ayoyi a majalisar dokokin Nijar | Siyasa | DW | 06.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabanin ra'ayoyi a majalisar dokokin Nijar

Har yanzu tsugunne ba ta kare ba a rikicin siyasar Nijar inda lamura ke cigaba da dagulewa musamman bayan zaben mambobin kwamitin zartarwar majalisar dokokin kasar

A jamhuriyar Nijar rikicin da ya hada bangaran 'yan adawa da takwarorinsu na bangaren masu rinjaye game da batun zaben wasu mambobin kwamitin zartarwar jamiyyar na ci gaba da yin kamari, wannan kuwa duk da hukuncin da kotun tsarin milkin kasar ta bayyana a kai

Sama da makonni biyu bayan soma zaben mambobin kwamitin zartawar majalisar, al'amura na ci gaba da dagulewa a zauren majalisar, inda sannu a hankali rikicin ke neman wuce makadi da rawa daga babin cacar baka zuwa na bacin juna dama neman kaiwa ga baiwa hammata iska.

Irin yanayin da mahawarar ke gudana ke nan a lokuta da dama a majalissar dokokin kasar ta Nijar.

Rikicin dai ya samu tushe ne bayan da wasu yan majalisar dokoki na bangaren adawa su ka ki amincewa da takarar mataimaki na biyu na shugaban majalisar dokokin, da rukunin nasu ya gabatar a bisa hujjar cewa rukunin nasu na ARN ya gabatar da takarar ba tare da kai masu shawara ba a bisa zarginsu da marawa gwamnati baya ba tare da lamanin uwar jamiyyun nasu .

Mafarin wannan rikici

To saidai a cewar Honnrable Zakari Amaru shugaban rukunin yan majalissar dokoki na bangaren masu rinjaye, da kuma ke marawa wasu takwrorinsu na bangaren adawa su 13 a cikin wanann rikici, shugaban majalisar dokokin na kasa Malam Hamma Amadu shine ummulhab'isan wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa.

To sai dai suma daga nasu bangare yan majalissar dokoki na bangaren adawa na ganin masu rinjaye ko kuma 'yan majority ne su ka haifar da wannan matsala ta hanyar yin katsalandan cikin harakokin cikin gidansu, kamar dai yadda Honorable SEIDU Bakari na jamiyyar Lumana Afrika ke cewa.

Niger Anschlag auf Hama Amadou Opposition

Hama Amadou shugaban majalisa na daga cikin wadanda ake zargi da rikicin siyasar kasar

To saidai yanzu haka ba duka aka taru aka lalace a majalissar dokokin ba inda wasu daga cikinsu su ka soma sa kira ga takwarorin nasu na ko wani bangare zuwa ga nuna halin dattaku;Honnorable Ahmed

Har ya zuwa karfe 12 na ranar yau yan majalissar ba su koma zaman nasu ba inda ko wane daga cikin bangarorin biyu ke can yana gudanar da taron gano bakin zaren warware matsalar.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin