1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Najeriya sun kubutar da Kiristoci 31 da aka sace

April 6, 2026

An sace mutanen da aka bukatar a wani kauye da ke da nisa kilomita 100 daga arewacin Abuja fadar gwamnati, duk da dimbin jami'an tsaro da aka girke a wuraren ibadar Kiristoci a lokacin bukukuwan Easter.

https://p.dw.com/p/5BjKB
Nigeria Schulkinder Entführung Armee
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kubutar da wasu masu ibada 31 da aka sace a yayin bukukuwan Easter a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar, sai dai ta ce wasu mutane biyar sun rasa rayukansu a yayin gumurzun da aka yi da maharan.

An sace mutanen ne a wani kauye da ke da nisa kilomita 100 daga arewacin Abuja babban birnin Tarayya, duk da dimbin jami'an tsaro da aka girke musamman a wuraren ibadar Kiristoci a lokacin bukukuwan Easter.

A cikin wata sanarwa, rundunar sojojin ta Najeriya ta ce ta samu wannan nasara ce ta hanyar kaukar mataki cikin gaggawa, sannan kuma dakarunta sun dakile wani hari da 'yan ta'adda suka yi yunkurin kai wa.

An sace sama da mutane 150 a Najeriya

Ko da yake sojojin sun ce an kai hari kan coci guda daya, amma rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida sun ce 'yan bindiga sun kai hari kan majami'u guda biyu, daya ta Katolika da kuma daya ta Evangelika, inda suka kashe akalla mutane takwas tare da sace wasu mutanen da dama.An sace sama da mutane 150 a Najeriya.