Rubutun Tafinag na Abzinawa | Amsoshin takardunku | DW | 17.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Rubutun Tafinag na Abzinawa

An dade ana amfani da rubutun Tafinag na Abzinawa a wasu assa na kasashen Sahel da ake samun Abzinawa.

Wannan rubutu na Tafinag na Abzinawa a wasu assa na kasashen Sahel musamman yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar da yankin arewacin Mali gami da wasu sassa na Libiya. A farko ana rubutun Tafinag daga hannu hagu zuwa dama ko kuma daga dama zuwa hannun hagu. Amma daga bisani an gyara inda ake rubutawa daga hannun hagu zuwa hannun dama.

Mata suna cikin wadanda suke bayar da taimako wajen bunkasa rubutun Tafinag na Abzinawa ke amfani da shi. Mata kan yi rubutun Tafinag a bakin rijiya domin ajiye sako ga wadanda za su zo. A kan rubuta misali cigiya na wani abu ya bata, ko kuma wani abu da aka tsinta. Rubutun Tafinag yana taka rawa wajen bunkasa harshen mutanen Abzinawa.