1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rikicin yankin Sahen ya raba daruruwan yara da matsugunansu

Binta Aliyu Zurmi
March 22, 2024

Akalla yara miliyan 1,800 ne rikici a kasashen yankin Sahel ya raba da matsugunansu a cewar wani rahoton kungiyar bada agaji ta Save the Children.

https://p.dw.com/p/4e0Cs
Welthunger-Index | Hungersnot in Madagaskar
Hoto: Tsiory Andriantsoarana/WFP/dpa/picture alliance

Rahoton wanda ya ce rikice-rikicen kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar a tsawon shekaru biyar ne ya yi sandiyar raba yaran da gidajensu.

Daga shekarar 2019 ya zuwa yau, binciken ya ce adadin yaran da suka tsere daga gidajensu ya karu daga dubu 321 ya zuwa miliyan 1.8

A cewar darakatar kungiyar da ke yankin na SahelVisha Snah, ta ce rikicin wanda aka manta da shi a yankin ya kasance daya daga cikin rikice-rikice mafi muni na jin kai a duniya.

Rahoton ya kara da cewar kasashen na Mali da Burkina Faso da Nijar sun jima suna fama da tashe-tashen hankula, ko baya ga haka suna fama da juyin mulki da ma fatara da ma sauyin yanayi.