Rikicin shugabanci na neman dara PDP gida biyu | Siyasa | DW | 05.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin shugabanci na neman dara PDP gida biyu

Kasa da makonni uku da gudanar da babban taro na kasa, rikici ya barke a cikin jam'iyyar PDP ta adawa a Najeriya da ke rabe a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar na Arewa da shugabancin rikon da ke tunanin dorewa.

Saurari sauti 03:04
Now live
mintuna 03:04

Rahoto kan rikicin shugabanci a PDP

A kauyuka da karkara ta tarayyar Najeriya 'ya'yan jam'iyyar PDP na kokarin zaben wakilansu a babban taro na kasa. Sai dai a Abuja babban birnin kasar rikici ne ke ci ganga-ganga, lamarin da ya kai ga raba lemar jam'iyyar zuwa gida gida. An dai share tsakar daren Laraba zuwa Alhamis ana ta taruka da nufin neman hanyar tinkarar matsalar da ke zaman karfen kafa.

Rabon mukamai a tsakanin sassan Najeriya da kuma daukar kujerar shugaban PDP ya zuwa sashen Arewa maso Gabas ne ya kai ga tada hankula musamman ma a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar na Arewa da ke karatun da biyu.

Dalilan neman dage babban taron PDP

Akalla sassa uku ne ke kiki-kaka cikin gidan wadata bisa makomar taron jam'iyyar da ke jagoranta ga adawa yanzu. Kuma akalla biyu a cikin sassan na da bukatar dage babban taro na kasar da uwar jam'iyyar ta tsara nan da makonni biyun da ke tafe.

Nigerianischer Präsident Goodluck Jonathan 11.11.2014

Tun bayan da tsohon shugaba Jonathan ya sha kaye a zaben 2015PDP ta shiga mawuyacin hali

Karkashin jagorancin Farfesa Jerry Gana ne 'ya'yan PDP na Arewa suka ce lokaci bai zo ba na babban taro, kuma hankali ya kamaci ya koma ga kokari na sulhunta tsakani maimakon neman samar da shugabanci a gari.

Gwamnonin Jihohin Ekiti da Rivers da ke Kudun ne dai ake yi wa kallon daurin gindi ga kokarin tabbatar da sabon shugabancin a Fatakwal a wani abin da 'yan Arewan ke kallon kokari na yankan baya ta Kudun.

Sai dai kuma in har 'ya'yan jam'iyyar suna tunanin hanyar kauce wa wala-wala, ga magoya bayan Shariff dai tunanin na zaman ginin jam'iiyar PDP da kowa ke iya yin alfahari kanta a nan a gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin