1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ina makomar alakar Riyadh da Abu Dhabi?

Mahmud Yaya Azare LMJ
December 31, 2025

Kasar Saudiyya ta sanar da wargajewar kawancenta da kasar Hadaddiyar Daular Labawa, na yaki da mayakan Houthi a Yemen.

https://p.dw.com/p/56AM5
Mayakan Yemen
Mayakan YemenHoto: Nabil Hasan/AFP

Wannan sanarwar da Saudiyya ta fitar na zuwa ne, bayan ita da gwamnatin Yeman sun zargi Hadaddiyar Daular Larabawan da yi musu zagon kasa a Yemen din ta hanyar goyan bayan 'yan awaren kudancin kasar da a yanzu haka sukai nasarar mamaye garuruwan Hadhar Maut da Maharah da ke kan iyakar Saudiyyan da Yemen, suke kuma barazanar kai wa kasar hare-hare.

Kakakin ma'akatar tsaron Saudiyya, ya kuma nuna kaduwar kasarsa da yadda kasar Hadaddiyar Daular Larabawan ta bayar da kofa ga makiyan kasarsa a Yemen: "..........tsaron kasarmu jan layi ne. Abun takaici ne a ce kasar Hadaddiyar Daular Larabawa za ta goyawa 'yan aware baya har ta ba su makaman da za su iya amfani da su kan Saudiyya........."

Lamura sun dagule tsakanin kasashen

Harin Saudiyya a Yemen
Harin Saudiyya a YemenHoto: Murad/Xinhua News Agency/picture alliance

Kafin hakan dai, sai da jiragen yakin Saudiyyan suka kai hari kan wasu jiragen ruwan Hadaddiyar Daular ta Larabawan biyu, yayin da suke sauke makamai a tashar ruwan Mukhallah da ke hanun 'yan awaren na Yeman, wadanda ke ta hankoron ballewa daga Yemen tun daga shekarar 1967, lamarin da ya kai ga barkewar yakin basasa a kasar da aka yi nasarar murkushe su a shekara ta 1990.

Tuni dai shugaban majalisar kolin kasar Yeman, Rashad Muhammad al-Alimi ya nemi kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa da ta kwashe dakarunta daga kasarsa cikin tsukin kwanaki biyu, inda ya ce da ma sun jima suna zargin kasar da yi wa kasarsu da ma Saudiyya zagon kasa: "Muna da tabbaci da dalilai na yankan shakku kan yadda Hadadddiyar Daular Laraba ta jima tana kitsa makarkashiyar wargaza Yemen ta hanyar goyan bayan 'yan awaren da ke daukar wasu yankunan Saudiyya a matsayin bangaren kasarsu da suke hankoran kafawa............"

Mataki na gaba

Harin Saudiyya a Yemen
Harin Saudiyya a YemenHoto: Murad/Xinhua News Agency/picture alliance

Tuni dai kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta nuna takaicinta da irin zafafan lafuzan da Saudiyya ta yi a kanta, tana mai musanta zargin yin barazana ga tsaron Riyadh din. Kana ta kara da nuna cewa, tuni ta fara kwashe dakarunta da suka rage a kasar ta Yemen. Abu Dhabin ta ce da ma tun a shekara ta 2019 ta kawo karshen zaman dakarunta da ke yakar matsalar ta'addanci a Yemen, kuma kadan daga ciki ne suka rage wadanda a cewarta su na sanya ido ne kan yanayin tsaron kasar da hadin gwiwa da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa.

A nasu bangaren mayakan na Houthi sun nuna jin dadinsu da matakin raba gari tsakanin Saudiyya da Hadaddiyar Daular ta Larabawa, suna masu fatan hakan zai taimaka wajen gaggauta yin sulhu tsakanin al'ummar Yeman karkashin dunkulalliyar kasa guda. Ana dai zargin Abu Dhabi da aiwatar da ajandar Isra'ila da wasu Kasashen Yamma ta raunata Kasashen Larabawa, ta hanyar kirkirar kungiyoyin 'yan aware masu dauke da makamai a kasashen Libiya da Sudan da ma kasar ta Yemen.

 

))