1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anfara taron G20 a Japan

Abdul-raheem Hassan
June 28, 2019

Batun kasuwanci da rikicin siyasa da sauyin yanayi kan gaba a jadawalin taron koli da shugabannin kasashen duniya mafi karfin tattalin arziki ke yi a birnin Osaka na kasar Japan.

https://p.dw.com/p/3LDhC
Japan G20 Gipfel Osaka Joko Widodo Präsident Indonesien
Hoto: President Secretary/Laily Rachev

Ana ganin rikicin kasuwanci tsakanin kasashen China da Amirka na zama wani batun da taron zai mayar da hankali a wannan shekara, amma da alama taron ya warware matsalar da ke tsakanin kasashen biyu. Da yake jawabi gabannin bude taron, Shugaban Amirka Donald Trump ya jaddada aniyarsa ta dakile tsarin network na G5 da katafaren kamfanin Chinan Huawei ke shirin kaddamarwa, da zai mamaye duniya. Firaministan Japan Shinzo Abe ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi amfani da damar taron domin sulhunta matsalolin da ke tsakanin kasashen da yakin kasuwanci domin samun cigaban kasuwanci irin na zamani.

Daga bisani ana sa ran tattauna batun sassauta takunkumin kasuwanci da kasar Amirka ta sawa Iran, bayan da suka samu sabanin ra'ayi kan yarjejeniyar nukiliya.