Rikicin kasafin kudi na kungiyyar Eu ya dauki hankalin taron kolin kungiyyar | Labarai | DW | 27.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasafin kudi na kungiyyar Eu ya dauki hankalin taron kolin kungiyyar

Faraministan kasar Biritaniya, wato Tony Blair ,wanda yanzu haka kasar sa ke rike da jagorancin kungiyyar Eu, yace yana fata kafin karewar wa´adin mulkin sa na jagorancin kungiyyar ta Eu a watan disamba yayan kungiyyar zasu cimma matsaya guda game da kasafin kudin kungiyyar da ake ta cece kuce akan sa.

Faraminista Blair ya fadi hakan ne kuwa a yau a lokacin da yake jawabi a gaban taron kolin kungiyyar na bayan fage da ake gudanarwa a wani katafaren zaure kusa da birnin London.

Wannan cece kuce dai ya samo asali ne a sakamakon rashin amincewar Biritaniya a gudanar da kwaskwarima a game da yadda take samun tallafi daga kungiyyar ta Eu indan anzo yin kaso na gaba daya.

A daya hannun kuma kasar Faransa tace ba zata yarda a soke irin tallafin da take samarwa manoman taba daga kungiyyar ta Eu , har sai an soke wancan tallafi da kasar ta Biritaniya ke samu.

Ba a da bayan wannan batu, ana sa ran shugabannin zasu tattauna batu na yadda za a samar da gidauniya don taimakawa ma´aikata dake