Rikicin jam′iyyar PDP ya ki ci ya ki cinyewa | Siyasa | DW | 18.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin jam'iyyar PDP ya ki ci ya ki cinyewa

Mabanbantan hukuncin kotuna da ake ci gaba da samu a Najeriya dangane da takaddamar shugabanci a babbar jam'iyyar adawa ta PDP, yana kara jefa jam'iyyar cikin rudu.

Tun bayan da jam'iyyar PDP ta sha kaye a babban zabe da ya gudana a bara, har yanzu jam'iyar da ta shafe shekaru 16 tana shugabancin Najeriya ta gaza dai-daita rikicin cikin gida da ya mamaye ta.

Tun bayan murabus din tsohon shugaban jam'iyyar Adamu Mu'azu, Sen. Ali Modu Sheriff da Sen. Ahmed Makarfi ke ta ja in ja a kan wanda zai dare kan kujerar shugabancin jam'iyyar.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin