Rikicin cikin gida a jam′iyyar PDP | Siyasa | DW | 03.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP

Wata sabuwa a jam'iyyar PDP ta kunno kai bayan da jami'an da ke yi mata aiki suka tada bore, lamari da ake ganin zai iya kaiwa ga nakasa jam'iyyar.

Kasa da watanni uku bayan da ta bar mulki, jam'iyyar PDP da ke zaman babbar jam'iyyar adawa a Najeriya na yunkurin kaiwa ga shiga rudu biyo bayan boren da jam'iyyar ta fuskanta daga masu yi mata hidima sakamakon kokarin da ta yi na rage yawan ma'aikata domin a cewarta ba ta da isassun kudin da za ta iya biyansu albashi.

Wannan hali na rashin kudi da jam'iyyar ta ce ta na ciki ya jawo yanke mata wuta da kuma ruwan fanfo da ake amfani da su cikin hedikwatar jam'iyyar ta gidan Wadata da ke tsakiyar birnin tarayya Abuja.

To sai dai ma'aikatan jam'iyyar sun ce wannan batu da ake na rashin kudi daidai ya ke da wasan yara domin kuwa ba zai yiwu PDP din ta yi kukan rashin kudi ba duba da irin kudin da ta tara lokacin yakin neman zabe.

Akalla ma'ikatanta 100 ne suka yi fito na fito da jam'iyyar inda suka nemi manyan jami'an jam'iyyar da su gaggauta ajiye mukamansu don a cewarsu ba abinda suka kitsa illa almubazzaranci da dukiyar da ke cikin lalitar jam'iyyar. Ma'aikatan har wa yau sun nemi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su gaggauta kaddamar da bincike don ladabtar da wanda ke da hannu kan wannan batu.

Sauti da bidiyo akan labarin