1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Aleppo ya kori dubban mutane daga gidajensu

Zainab Mohammed Abubakar
January 16, 2026

Mahukuntan Siriya sun ce kimanin mutane 4,000 ne suka tsere daga garuruwan Deir Hafir da Maskana a wannan Juma'ar (16.01.2026).

https://p.dw.com/p/56ySm
Hoto: Omar Haj Kadour/AFP/Getty Images

Dubban mutane sun tsere daga yankunan gabashin Aleppo, biyo bayan tsanantar fada tsakanin sojojin gwamnati da mayakan SDF wadanda akasarinsu Kurdawa ne.

A makon da ya gabata ne dai fada mai tsanani ya barke a gundumomin Aleppo da Kurdawa ke iko da su, a yayin takaddama kan shirin hada gwamnatocin Kurdawa masu cin gashin kansu a tsarin gwamnatin Siriyar. Kuma daga karshe gwamnatin rikon kwarya ta mayar da unguwannin Kurdawa na Aleppo karkashin ikonta.

A yanzu haka dai sojojin gwamnati suna kokarin fatattakar mayakan SDF zuwa yankin gabashin kasar, inda har yanzu suke iko da manyan garuruwan kasar. A lokacin yakin basasar Siriya, ana daukar SDF a matsayin babbar kawar Amurka a yaki da Kungiyar IS mai akidar kafa daular musulumci.

Har yanzu ba a aiwatar da yarjejeniyar sanya SDF cikin rundunar sojojin gwamnati ba, tun bayan hambarar da gwamnatin sai Madi ka ture na Bashar al-Assad.