1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Amurka ta kai hare-hare kan kungiyar IS a Siriya

December 20, 2025

Jami'an Amurka sun ce sun kai hare-haren ne a matsayin ramuwar gayya, bayan kashe sojojinta biyu a makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/55kJl
Amurka ta kaddamar da hare-hare kan kungiyar IS a Sirirya
Amurka ta kaddamar da hare-hare kan kungiyar IS a SiriryaHoto: U.S. Air Force/REUTERS

Amurka ta sanar da kai hare-hare ta sama kan wasu wuraren fiye da 70 na 'yan kungiyar IS a Siriya. Rahotanni sun yi nuni da cewa, Amurka ta kai hare-haren ne a matsayin ramuwar gayya bayan kashe mata sojojinta biyu da kuma wani mai fassara a Palmyra a makon da ya gabata. Rundunar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, ta ce sojojinta sun fara kai farmaki ne domin lalata makaman IS da sansanoninsu da kuma muhimman gine-ginensu.

Karin bayani: Sojojin Amurka sun kai jerin hare-hare a Siriya

Gidan talabijin na gwamnatin Siriya ya ce, hare-haren sun shafi yankunan karkara na Deir ez-Zor da Raqqa, da kuma yankin Jabal al-Amour. A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce kaddamar da hare-haren ba sabon yaki ba ne, sai dai an tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro. Ya kara da cewa sojojin Amurka sun kashe mayakan IS da dama kuma za su ci gaba da kai musu hari.