1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Kurdawa sun fice daga yankin Aleppo na kasar Siriya

Binta Aliyu Zurmi
January 11, 2026

Dakarun Kurdawa sun fice daga birnin Aleppo bayan shafe kwanaki ana gwabza kazamin fada tsakaninsu da sojojin gwamnati.

https://p.dw.com/p/56deh
Syrien Aleppo 2026 | Evakuierung von YPG/SDF-Kämpfern aus dem Viertel Sheikh Maqsoud nach Tabka
Hoto: Arif Hudaverdi Yaman/Anadolu/picture alliance

Kamfanin dillancin labaran Syria da wani kwamandan Kurdawa sun ce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Yarjejeniyar da ake sa ran za ta kawo karshen fada tsakanin dakarun Kurdawa da sojojin Siriya.

Ana kwashe mayakan na Kurdawa cikin motocin safa-safa zuwa yankin arewa maso gabashin kasar da ke karkashin ikon Kurdawa.

A ranar Talata da ta gabata ce rikici ya barke a tsakanin bangarorin biyu. Akalla mutane 22 ne suka mutu a rikicin sannan sama da 140,000 suka rasa matsugunansu a Aleppo.