Ricikicin MNSD Nasara na daukar dimi | Siyasa | DW | 25.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ricikicin MNSD Nasara na daukar dimi

A Jamhuriyar Nijar lokacin dab ya rage watanni uku a gudanar da zaben shugaban kasa, rikicin cikin gida a jam’iyyar MNSD NASARA ya dauki wani sabon salo inda kwamitin kolin jam'iyyar ya kori wasu membobinsa

Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar ta MNSD NASARA ya gudanar ya dauki matakan ladabtarwa dabam-dabam a kan wasu kusoshin jam’iyyar 16 a bisa zarginsu da rashin da’a da yin tawaye da kuma yin karan tsaye ga dokokin jam’iyyar. Wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar ta MNSD NASARA guda biyar da aka kora akwai tsohon minista Abdulkadri Tidjani wanda da ma jam’iyyar ta sa aka cire shi daga mukaminsa na minista da Abdouraouf Dodo da Issoufou Tamboura da Chetima Hassane da kuma musamman Honnorable Mourtala Alhaji Mamaouda shugaban rukunin 'yan majalisar dokoki karkashin inuwar jam'iyyar a majalisar dokokin Nijar, wanda a kuma a cewarsa jam’iyyar ta dauki wannan mata ki ne kansu dan kawai sun bukaci a kawo gyara wajen tafiyar da shugabancin jam’iyyar a yayin da yake martani kan hukuncin uwar jam'iyyar.

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta MNSD ya ce kofofinsa a bude suke ga duk wadanda aka dauki matakin kansu idan har sun yi nadamar abin da suka yi sun kuma amince komawa ga yi wa dokokin jam’iyyar biyayya, wannan rikici na jam’iyyar MNSD NASARA babbar abokiyar kawancen mulki wacce a baya ta mulki Nijar a karkashin jagorancin Shugaba Tanja Mammadou na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage watanni uku a gudanar da zaben shugaban kasa.