1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha tana shirin tsagaita wuta bayan luguden wuta a Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou SB
March 7, 2022

Bayan luguden wuta a yankin Kharkiv na Ukraine, rundunar tsaron Rasha ta bayyana shirin tsakgaita buda wuta a wani mataki na ficewa da fararen hula da yaki ya rutsa da su.

https://p.dw.com/p/486WR
Russland-Ukraine Krieg | Bombenangriff in Irpin
Hoto: Emilio Morenatti/AP Photo/picture alliance

A yayin da jiragen sojan Rasha suka yi luguden wuta a daren Lahadi zuwa wannan Litinin kan birni na biyu mafi girma a Ukraine Kharkiv, sannu a hankali dakarun tsaron Rasha na kokarin yi wa babban birnin kasar Ukraine Kiev kawanya a lokacin da ake hasashen tawagogin kasashen biyu za su sake tozali da juna don ci gaba da tattauna batun tsagaita wuta a karo na uku.

Rundunar tsaron Rasha ta bayyana shirin tsakaita buda wuta a wasu sassan Ukraine a wannan Litinin, da zummar kai agajin gaggawa ga fararen hula da yaki ya rutsa da su. Sanarwar da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar ta ce matakin tsagaita wutar zai shafi Kharkhiv da Kiev da Marioupol da Soumy, a wani yunkuri na ficewa da fararen hula ke yi.