1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da China na shirin gagarumin atisayen soji

Abdoulaye Mamane Amadou
September 1, 2022

Rasha ta sanar da shirinta na kaddamar da wani gagrumin atisayin soji mafi girma da ta yi wa lakabi da Vostok-2022 a makon gobe a daidai lokacin da take cigaba da mamayar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4GKg4
Krim Einmarsch Russland Ukraine Soldaten Z Symbol
Hoto: Sergei Malgavko/TASS/dpa/picture alliance

Fadar mulki ta birnin Moscow ta gayyaci kasar Sin a yayin gagarumin atisayin wanda hakan ke kara tabbatar da kusantar kasashen biyu da ke takon saka da manyan kasashen yammacin duniya, kana kuma ana sa ran ko baya ga China ana sa ran wasu makwabtan kasar irin su Belarus Siriya da Indiya ka iya halartar atisayin.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta wallafa wasu hotunan da ke nuna dakarun sojanta na shirin atisayin ta sama da kasa, inda za su koyi kare kai daga hare-haren makamai masu linzami, ko kuwa luguden wuta kan abokan gaba masu amfani da manyan tankokin yaki. Moscow ta ce fiye da sojoji dubu 50 ne za su shiga atisayin, kan wasu makamai akalla dubu biyar da jiragen yaki 140 baya ga na ruwa kimanin 60.